Za mu samu gagarumin rinjaye — Suu Kyi

Hakkin mallakar hoto EPA

Jagorar jam'iyyar adawa a kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta shaida wa BBC cewa tana sa ran jam'iyyarta za ta lashe kashi uku cikin hudu na kujerun majalisar dokokin kasar.

Sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadi na ci gaba da fitowa a hankali, kuma kalamin nata ya yi daidai da wasu sakamako da aka samu inda jam'iyyarta National League for Democracy ta lashe kujeru 78 cikin 88 na majalisar dokokin.

A hirarta ta farko tun bayan fara kada kuri'a, Ms Suu Kyi ta ce ta tabbatar sojoji ba za su yi kafar-ungulu ga zaben ba.

Za a iya kwashe 'yan kwanaki kafin a fitar da sakamakon karshe na zaben.