Lokaci ya yi da Najeriya za ta maida hankali a kan noma

A Najeriya wasu al'ummar kasar na ci gaba da bayar da shawarwari kan yadda za a bunkasa harkar noma da kuma kasancewar noman wani ginshikin tattalin arzikin kasar, kamar yadda ya kasance a baya.

Da dama daga cikin 'yan kasar na gani samun man fetur a kudancin kasar shi yasa 'yan arewa su ka yi wa harkar noman rukon sakainar kashi, to sai dai yanzu kuma lokaci ne da ya kamata a rungumi noman hannu biyu.

Sun yi kira da gwamnatin kasar ta ta kara kaimi wajen samar wa manoma da tallafi da kuma taki domin ta wadannan hanyoyi ne fanin noma zai bunkasa a kasar.

A baya dai gwamnati ta bulo da wani tsari na samar wa manoma da taki ta hanyar amfani da wayar salula kuma wasu 'yan Najeriya sun ce shirin ya yi tasiri sosai wajen taimakwa manoma.