Dakarun Syria sun samu galaba kan IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun da ke goyon bayan shugaba Assad

Gidan talabijin na kasar Syria ya ce dakarun gwamnati sun rusa kofar ragon da 'yan kungiyar IS suka yi wa wani muhimmin sansanin sojin sama da ke lardin Aleppo a arewacin kasar na tsawon shekaru biyu.

Wani mai daukar hoton kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce sojojin sun kutsa kai cikin layin da 'yan bindigar IS suka shata a filin jirgin sama na Kweyris -- inda suka cimma sojojin gwamnati da ke ciki.

Rukunin sojojin sun tuntubi dakarun da ke kare sansanin sojin saman sannan suka kawar da 'yan gwagwarmaya da yawa.

Wani wakilin BBC ya kwatanta shigar ta su a matsayin wata babbar nasara ga sojojin Syria.

Wata da watanni dakarun sojin Syrian ba sa samun nasara amma a 'yan makonnin nan sun fara samun nasara saboda taimakon sojojin Rasha.