Amurka ta sa tikwuici kan 'yan al-Shabab

Image caption Kungiyar al-Shabaab na ci gaba da yaki da gwamnatin Somalia.

Gwamnatin Amurka ta sha alwashin bayar da tikwuicin dala miliyan 27 ga duk wanda ya bata labarin yadda za ta kama shugabannin kungiyar al-Shabaab guda shida.

Tikwuicin da ya fi girma shi ne na dala miliyan wanda aka sanya a kan shugaban kungiyar Abu Ubaidah.

Ubaidah ya maye gurbin Ahmed Abdi Godane, wanda harin da jirgin saman Amurka maras matuki ya kai ya yi sanadiyar mutuwarsa a bara.

Mahad Karate, wanda aka fi sani da Abdirahman Mohamed Warsame na cikin 'yan kungiyar da aka fi nema ruwa-a-jallo saboda zargin da ake yi masa da hannu a harin da aka kai kan wata Jami'ar Kenya, lamarin da ya kai ga mutuwar a kalla mutane 148.

Kungiyar ta Al-Shabaab na ci gaba da yaki da gwamnatin Somalia wacce Amurka ke mara wa baya.