Sabbin ministocin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

A yau Laraba Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai rantsar da sabbin ministocin gwamnatinsa kusan watanni shida bayan karbar ragamar mulkin kasar.

Ana sa ran bayan bukin rantsarwar, shugaban ya kaddamar da majalisar zartarwar ta hanyar jagorantar zaman farko da sabbin ministocin nasa.

Sai dai shugaban Buhari ya ce ba dukkanin ministocin ne za su samu mukaman shugabantar ma'aikatu saboda karancin kudaden gudanar da gwamnati.

A ranar Talata ne dai shugaban kasar Najeriya ya nada wasu sabbin sakatarorin gwamnati bayan da ya kori wasu.