Jami'in manhajar KakaoTalk ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manhajar sada zumunci ta KakaoTalk

Daya daga cikin mutanen da suka kirkiro manhajar sada zumunci ta KakaoTalk ya yi murabus bayan an zarge shi da kasa hana yada hotunan cin zarafin yara ta manhajar.

Kamfanin ya sanar da murabus din Lee Seok-Woo, mako daya bayan masu tuhuma na gwamnati sun same shi da laifi, sai dai ba a tsare shi ba.

Mista Lee ne shugaban kamfanin manhajar KakaoTalk har zuwa watan Agusta, lokacin da ya koma matsayin mai bada shawara a kamfanin.

Kamfanin ya ce fiye da mutane miliyan 100 ne ke amfani da manhajarsa ta sada zumunta KakaoTalk.

Manhajar ta KakaoTalk ta na bai wa mutane damar yin magana da juna, a dai-dai-ku, ko a cikin gungu, kuma ta na ba su damar yada hotuna, ko bidiyo.

Kamfanin ya ce yana daukan mataki na ganin ba a yada abubuwan da aka haramta a kasar.

Samun Mista Lee da laifi da aka yi cikin makon jiya shi ne karo na farko da hukumomi a kasar Koriya ta Kudu suka tuhumi wani jami'in kamfanin sadarwa ta intanet da laifin karya dokar dake kare kananan yara daga cin zarafin lalata a kasar.