Kai Tsaye: Rantsar Da Ministocin Nigeria

Latsa nan domin sabunta shafin

Barka da zuwa shafin BBC Hausa kai tsaye a kan bikin rantsar da sabbin ministocin Nigeria, karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Hakkin mallakar hoto AP

Za ku iya aiko mana da ra'ayoyinku ta e-mail hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta WhatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

12:27 Kemi Adeosun - Ministar Kudi, Raji Fashola - ministan makamashi da ayyuka da samar da gidaje, Rotimi Amaechi - Ministan Sufuri, Mohammed Bello - Ministan Abuja. Solomon Dalung - Ministan wasanni da matasa. Audu Ogbeh - Ministan harkokin ayyukan gona.Ogbonnaya Onu- ministan kimiyya da fasaha. Adamu Adamu - Ministan Ilimi.

12:15 Ra'ayoyin 'yan Najeriya a BBC Hausa Facebook:

Usman Mohammed Maiduguri "To ina kira ga ministocin baba Buhari su tabbata sun yi wa talakawan Najeriya aiki tsakaninsu da ALLAH."

Abubakar Ochohun Abdulmalik " lhamdulillah, yanzu sai a gaggauta bai wa miliyoyin matasan Najeriya aikin yi ba tare da bata lokaci ba."

Isuhun Diyla Pakì "To sabbin ministocin Najeriya 36 mu na taya ku murnar shan rantsuwar kama aiki, Allah ya taya ku riko ya ba ku ikon tafiyar da jagoranci nagari amin."

Samaila Gusami "To ina kira ga ministocin baba Buhari da su rike gaskiya da amana a kan mulkin da aka ba su. Su yi jagorancin al'uma da aka ba su nagari da fatan Allah ya taimaka musu."

12:05 An kammala rantsar ministocin Najeriya. Kashi na karshe da suka sha rantsuwa su ne Aisha Abubakar daga jihar Sokoto da Aisha Alhassan daga jihar Taraba da Hajia Khadija Bukar Ibrahim daga jihar Yobe da kuma Mansur Dan Ali daga jihar Zamfara.

Hakkin mallakar hoto NTA

11:56 Za a rantsar da kashi na karshe na ministoci hudu daga jihohin Sokoto da Taraba da Yobe da kuma Zamfara.

11:50Isaac Adewole daga jihar Osun da Barrister Adebayo Shittu daga jihar Oyo da Solomon Dalong daga jihar Plateau da kuma Rotimi Amaechi daga jihar Rivers sun sha rantsuwa. Su ne kashi na takwas a cikin ministocin da Shugaba Buhari ya rantsar.

11:37 Kashi na bakwai na ministocin da suka sha rantsuwa sun hada da; Ibrahim Usman Jibrildaga jihar Nasarawa da Abubakar Bawa Bwari daga jihar Niger da Kemi Adeosun daga jihar Ogun da kuma Cladius Daramola daga jihar Ondo.

11:25Abubakar Malami daga jihar Kebbi da James Ocholi daga jihar Kogi da Lai Mohammed daga jihar Kwara da kuma Babatunde Fashola daga jihar Lagos sun sha rantsuwar kama aiki.

11:15 Ana ci gaba da rantsar da sabbin ministocin Najeriya. Kashi na shida na wadanda za a rantsar sun fito ne daga jihohin Kebbi da Kogi da Kwara da kuma Lagos.

11:10Suleiman Adamu daga jihar Jigawa da Zainab Shamsuna Ahmed daga jihar Kaduna da Abdulrahman Dambazau daga jihar Kano da kuma Sanata Hadi Sirika daga jihar Katsina suma sun rantse da Kur'ani a kan cewar za su yi aiki babu san zuciya a matsayin ministocin Najeriya.

Hakkin mallakar hoto NTA

11:00 Kashi na biyar na ministocin sun fito ne daga jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da kuma Katsina.

10:55 Kashi na hudu na ministocin da suka sha rantsuwa sun hada da; Kayode Fayemi daga jihar Ekiti da Geoffrey Onyemadaga jihar Enugu da Amina Mohammed daga jihar Gombe da kuma Farfesa Anthony Onwuka daga jihar Imo.

10:47 Ministoci daga jihohin Ekiti da Gombe da Enugu da Imo da kuma Gombe.

10:40Pastor Usani Uguru daga jihar Cross River da Ibe Kachikwu daga jihar Delta da Ogbonaya Onudaga jihar Ebonyi da kuma Osagie Ehanire daga jihar Edo.

Hakkin mallakar hoto NTA

10:33 Kashi na uku na ministocin da za rantsar sun fito ne daga jihohin Cross Rivers da Delta da Ebonyi da kuma Enugu.

10:28 Kashi na biyu na ministocin da suka sha rantsuwa su ne; Heineken Lokpobiri daga jihar Bayelsa da Adamu Adamu daga jihar Bauchi da Cif Audu Ogbeh daga jihar Benue da kuma Mustapha Baba Shehuri daga jihar Borno.

10:23 Karin ministoci hudu sun sha rantsuwar kama aiki. Kafin kowannensu ya sha rantsuwa sai an gabatar da takaitaccen tahirinsa.

Hakkin mallakar hoto NTA

10:19 An kira Sanata Heineken Lokpobiri da kuma Adamu Adamu domin su sha ratsuwa.

10:14Okechukwu Enelamah daga jihar Abia, da Muhammed Bello daga jihar Adamawa, da Sanata Udoma Udo Udoma da Sanata Chris Ngige daga jihar Anambra sun sha rantsuwar kama aiki.

10:10 An gabatar da ministoci hudu daga jihohin Abia da Adamawa da Akwa Ibom da kuma Anambra.

10:00 An yi taken Najeriya sannan mai bai wa shugaban kasa shawara ta fuskar harkokin yada labarai, Garba Shehu ya yi gaisuwa kafin ya bayyana cewar za a soma rantsar da ministocin.