Shugaban Myanmar ya taya Suu Kyi murna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al'ummar Myanmar suna murnar zabe

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein ya taya jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi murna a kan nasarar da suka samu a zaben da a ka yi ranar Lahadi.

Jam'iyyar NLD ta Ms Suu Kyi ta samu kusan kashi casa'in cikin dari na kujerun majalisar da aka bayyana kawo yanzu.

Ms Suu Kyi ta rubutawa mahukuntan kasar wasika a kan cewa ya kamata su zauna domin dai-daitawa.

Amma kuma mai magana da yawun mahukuntan U Ye Htut ya ce ba za a zauna wani taro ba har sai an sanar da sakamakon zabe na karshe.

Ya kuma hakikance cewa ba za a bata lokaci ba wajen sanar da sakamakon zaben.

Ms Suu Kyi na yin taka-tsan-tsan duk da irin gagarumar nasarar da jam'iyyarta ta samu.

Jam'iyyar NLD ta samu gagarumar nasara a zabukan shekarar 1990, amma kuma sai aka soke shi, sannan ita kuma a ka yi mata daurin talala na tsawon lokaci.

Jam'iyyar USDP ta shugaba Thein Sein ta samu kaso biyar cikin dari ne na kujerun majalisar da a ka bayyana kawo yanzu.