Niger ta ce taimakon turai yayi kadan

Mahamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto

Shugaban Niger, Mahamadou Issoufou ya ce gaskiya ne kasashen turai sun gabatar da shawara ta kafa asusu na Euro Biliyan daya da miliyan dubu dari takwas.

To saidai ya kara da cewar kasashen turai sun amince akan cewar wannan kudi ba zai isa ba, idan aka yi la'akari da gagarumar matsalar, don haka ya zama wajibi, wasu ma su kara kawo tasu gudunmowar.

Shugaban ya ce kasashen Africa basu je wajen wannan taro da kokon bara ba, yana mai cewar wajibi ne kasashen su yi aiki a matsayin abokan kawance da kasashen turai wadanda suka san hakkin da ya rataya a wuyansu domin aiwatar da yarjejjeniya akan dukkanin matsalolin da suke fuskantar mu.

Mamadou Issoufou ya ce a matsayin kasar da mutane suke yada zango kamar Niger, akwai bukatar mu dauki wasu matakai na tsaro domin takawa bakin haure burki da karesu da kuma kafa wasu cibiyoyi na karbar baki.

A shirye muke mu in ji shi mu samar da irin wadannan cibiyoyi a kasashenmu, domin mu tunkari kungiyoyi masu fasakwabrin bakin haure. Irin wadannan kungiyoyi a lokutta da dama suna da alaka da kungiyoyi masu faskwabrin miyagun kwayoyi, ko bakin haure ko kuma ma kungiyoyin 'yan ta'adda.