PDP za ta yi taron farfado da kanta

A Najeriya babbar jam'iyar adawa ta PDP za ta gudanar da wani taron ta na kasa

Taron dai zai gudana ne domin sakewa jam'iyar wani sabon fasali, abinda kuma 'ya 'yan jam'iyyar ke ganin zai dawo da kimar jam'iyyar da kuma martabar ta ga idon 'yan Najeriya.

Ana sa ran taron zai kawo karshen kiki-kakar da jam'iyyar ke fuskanta da kuma fatan dinke barakar da ake ganin ta kunno kai cikin jam'iyyar.

PDP ta kuma nemi gafarar 'yan Nigeria bisa kura-kuran da ta tafka a shekarun da ta shafe ta na mulkin Nigeria.