Sony zai daina sayar da kassete na Betamax

Kamfanin Sony ya yi shellar cewa zai daina sayar da kassete na bidiyo da aje kira Betamax daga watan Maris na shekara ta 2016.

Kamfanin ya bayyana haka ne a shafinsa na internet cewa zai kuma daina fitar da karamin kassete din da ake amfani a cikin bidiyo da ke nadar hoto watau Micro MV .

Kamfanin be sake kera wata kamera da za a saka kassete din Micro MV a ciki ba tun a shekara ta 2005.

A shekara ta 1975 ne kamfanin Sony ya kaddamar da kassete din kafin abokin gogayarsa watau JVC ya kaddamar da kassete din VHS.

Sai dai duk da cewa mutane da dama na ganin Betamax ta fi inganci amma wasu sun ce kassete din VHS sun fi daukar abu har na tsawon lokaci