'Yan Boko Haram sun kashe mutane 25 a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Jamhuriyar Nijar sun mayar da martani.

Wasu mahara da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 25 a harin da suka kai a wani kauye da ke yankin Bosso.

Dakarun sojin Nijar sun mayar da martani inda suka kashe 'yan kungiyar 20 suka kuma kori wasu.

Lamarin ya faru ne ranar Laraba.

Yankin na Bosso yana kan iyaka da Najeriya.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta kara kaimi a hare-haren da take kai wa a wasu yankuna a Jamhuriyar Nijar.

Yankin na Bosso yana kan iyaka da Najeriya.