An yi luguden wuta kan 'Jihadi John'

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Jihadi John

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce jiragen saman Amurka sun yi luguden wuta a maboyar dan kungiyar IS din nan, Jihadi John, kuma tana da yakini sun kashe shi.

Jihadi John, dan kungiyar IS ne wanda yake fitowa a bidiyon da kungiyar ke fitar wa da ke nuna yadda mayakan kungiyar ke fille kawunan turawan da take garkuwa da su.

A cewar ma'aikatar tsaron ta Pentagon, dakarun Amurka sun kai farmakin ne ranar Alhamis a kusa da birnin Raqqa na Syria.

Wani kakakin ma'aikatar, ya ce suna tantance sakamakon farmakin domin tabbatar ko an kashe Jihadi John.

Shi dai Jihadi John -- wanda aka bayyana a matsayin dan rajin jihadi da ya fito daga Burtaniya -- sunansa na gaskiya shi ne Mohammed Emwazi.

Ya bayyana a hotunan bidiyo da dama na kungiyar IS da ke nuna yadda take kashe mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su.