Ministocin Nigeria sun fara aiki

Image caption Buhari ya bukaci ministocin su yi aiki domin kyautata rayuwar 'yan Najeriya.

Wasu ministocin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar ranar Laraba sun fara aiki jim kadan bayan sun saba-laya.

Rahotanni daga ma'aikatar makamashi da ayyuka da gidaje na cewa sabon ministan ma'aikatar, Babatunde Fashola, ya shiga ofis jim kadan bayan rantsar da shi, inda ya gana da manyan jami'an ma'aikatar da sauran ma'aikata.

Kazalika, karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu ya soma aiki a ma'aikatar, inda ya bayyana wa manema labarai irin alkiblar da zai fuskanta.

Ita ma ministar muhalli, Hajiya Amina Mohammed, wacce ta yi wa 'yan jarida jawabi a yayin da ta isa ma'aikatar, ta sha alwashin yin bakin kokarinta domin kawo sauyi wajen inganta muhalli.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi kira ga ma'aikata da su zage-dantse wajen yin ayyukan da aka ba su, yana mai cewa ba zai yarda da sakaci da bambadanci ba.

Sauran ministocin da suka fara aiki sun hada da ministan kwadago da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige da takwaran aikinsa na birnin tarayya, Abuja, Alhaji Mohammed Bello da na ma'aikatar kula da yankin Neja Delta, Pastor Usani Uguru da ministar kudi, Folakemi Adeosun.