Facebook ya kaddamar da manhajar "Notify"

Image caption Manhajar mai bayar da labarai iri-iri

Shafin sada zumunta na Facebook ya kaddamar da wata manhaja ta wayoyin iPhone wadda ake kira "Notify", wadda za ta rika tattara labarai da nishadi wuri daya, domin kawo wa masu wayoyin a kai a kai.

Tashoshin labarai na CNN da Fox News da jaridar Washington Post suna daga cikin kafofin yada labarai 70 da za su rika samar da labarai ga manhajar.

Duk wanda ya sanya manhajar a wayarsa, zai iya zaban hade-haden labaran da ya ke so manhajar ta rika kawo masa.

Manhajar za ta yi gogayya da Twitter da kuma tsarin samar da labarai na Apple News wadanda suke kawo labarai da dumi-duminsu.

Mutane za su iya tsara manhajar ta Notify ta yadda za su kebe irin labaran da suke so, ko na fina-finai, ko wakoki, ko labaran wasanni, ko kuma labarai a kan taurarin 'yan wasa.

A yanzu, ana samun manhajar Notify ce a tsakanin masu amfani da shafin Facebook a wayoyin iPhone a Amurka.

Shafin na Facebook bai fadi lokacin da zai fadada amfani da manhajar zuwa sauran sassan duniya ba, da kuma sauran nau'o'in wayoyi.