Hamada tana neman korar mutane daga muhallansu

Image caption "Mu a nan hanyar cin abincin mu na ga noma, idan kuma hanyar ta baci mun shiga uku" In ji Amadou Souare

Majalisar Dinkin Duniya ta yi wani hasashe cewa za a tilastawa mutane sama da miliyan 50 barin muhallansu nan da shekarar 2020, saboda hamada za ta mamaye kasashen su, kamar yadda ya riga ya fara faruwa a Senegal.

Khalidou Badara, wani makiyayi ne da ya kai wakiliyar BBC Laeila Adjovi wani tudu a garin Louga na arewacin Senegal, inda ya bayyana mata yadda hamadar ta sauya yankin.

Ya ce, "lokacin ina yaro, ba na ma soma tunanin cewa zan hawo nan wurin saboda ciyayi da bishiyoyin da ke dankare a wurin, amma 'yan shekarun da suka wuce guguwa da yashi duk sun mamaye wurin".

Ya kara da cewa, "Kusan babu sauran bishiyoyi, kuma ciyayi ba sa girma a nan, saboda haka duk shekara muna kara nesanta daga nan domin mu nemi inda shanun mu za su samu abinci".

Rayuwarsu ta shiga matsanancin hali a yanzu saboda mamayar da hamada ke kara yi.

Ba Khalidou ne kadai ke da irin wannan korafi ba, Majalisar Dinkin Duniya ta ce hamadar ta shafi mutane biliyan daya da rabi, a duniya baki daya.

Wasu ayyuka da mutane kan yi masu gurbata fasalin kasa da kuma sauyin yanayi sune ke haddasa gurgusowar hamada.

'An rasa kasa'

A cewar alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ke fitarwa, a kowacce shekara ana rasa filin noma kimanin hekta miliyan 12, inda da za a iya noma hatsi tan miliyan 20.

Image caption Cheikhou Lo ya ce aiki ya tsaya saboda shigowar hamada.

Dole ta sa al'ummun da lamarin ya shafa su yi kaura, kamar yadda Cheikhou Lo, wani mazauni a wani bangare na garin Louga, a kauyen da ake kira ya shaida wa Laeila.

Image caption Cheikhou Lo's ya ce shukar da suka yi ta gyada ta baci wannan shekarar.

Ya yi shukin gyada da wake da fatan zai samu riba bayan ya sayar, amma karancin ruwan sama da kuma zagwanyewar kasar ya sanya shukar rashin tsirowa.

Ya ce "A shekarun baya muna girbi dayawa saboda akwai yawan ruwan sama, har ma mu kai wani kakar damunar muna amfani da abincin da muka girbe. Yanzu da fari ya shigo ba za mu iya aiki ba"

Image caption A baya Senegal ta fi samun ruwan sama da damuna.

'Neman mafita'

Akwai dai wani shiri da wata kungiya da ake cewa The Green Wall initiative ta ke gudanarwa, wanda ke yunkurin dakile shigowar hamadar, ta hanyar sanya shingayen shuka a wuraren da hamadar ta fi shafa a nahiyar Afrika, kamar daga Senegal zuwa Djibouti.

Kungiyar ta ce an shuka daruruwan bishiyoyi a yankunan, kuma sun kyautat zaton shingayen bishiyoyin da za'a shuka a Senegal kadai za su kai tsawon kilomita 545, wata mil 338.

Image caption Al'umma dai ba lallai su jira har shekaru goma kafin shukan ciyayi da bishiyoyin su tsiro ba.

Bayan haka kuma kungiyar tana taya makiyaya da manoma ajiyar kudin adashi, da kuma shuka kayyakin kara lafiya, haka zalika tana koyar wa yara amfanin kare muhallansu.