An kwato migayun kwayoyi a Kano

Jami'an tsaro a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce sun kwato muggan miyagun kwayoyi masu dimbin yawa a hannun wasu mutane.

An gano inda ake boye kwayoyin ne a fitacciyar kasuwar nan ta Sabon Gari, da kuma cikin wasu shaguna biyu a unguwar Ja'en da ke birnin Kano.

An kama mutane 28, cikin su har da wata mace guda daya, da ake zargi da laifukan.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, rundunar 'yan sanda a Kano ta matsa kaimi wajen kawar da masu aikata munanan laifuka a jihar.