Kai Tsaye: Hare-hare a Faransa

Latsa nan domin sabunta shafin

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

20:41 Jami'ai a Faransa da ke binciken hare haren da aka kai a Paris sun ce maharan sun tsara kan su ne zuwa kungiyoyi uku.

Kungiyar masu da'awar jihadi ta ce ita ce ta kai harin na ranar Juma'a.

Babban lauyan Faransa mai gabatar da kara Francois Molins yace maharan bakwai ne aka kashe ba takwas ba kamar yadda aka bada rahoto a baya.

Yace dukkaninsu suna dauke da bindigogi samfurin Kalashnikov da kuma jigidan bama bamai na kunar bakin wake.

Mutane 129 aka kashe wasu 352 kuma suka jikata. Daya daga cikin maharan mazaunin Paris ne kuma an san shi da aikata munanan laifuka a baya.

Hakkin mallakar hoto AFP

17:09 Ana kara samun bayanai akan asalin wasu daga cikin mutanen da suka kai harin Paris.

An ruwaito yan sandan Faransa su na cewa sun gano daya daga cikin maharan dan Faransa wanda kuma ke da alaka da yan ta'adda.

Yayin da kuma aka gano Faspo din Syria kusa da gawar wani dan bindigar.

Wani ministan Girka ya ce mai Faspo din ya wuce ta kasar Girka a cikin watan Oktoba.

A wani ci gaban kuma yan sanda a Belgium sun kai samame a wurare da dama a Brussels game da hare haren.

Ministan shari'a na Belgium yace an kama wasu mutane.

Hakkin mallakar hoto Sbastien GEORIS RTBF

15:48 Kasashe da dama na tarayyar turai sun tsaurara tsaro bayan harin da aka kai a Paris.

Kasashen Italiya da Belgium sun tsaurara tsaro a kan iyakokinsu da Faransa.

Firayiministan Belgium Charles Michel ya gargadi yan kasarsa su guji zuwa Paris a yanzu.

A Poland ministan harkokin tarayyar turai mai jiran gado Konrad Szymanski yace saboda tashin hankalin da ya faru a Faransa, kasarsa ba za ta karbi kason yan gudun hijira da kungiyar tarayyar turai ta ce za ta rarraba ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

15:37 Gwamnatin Faransa ta tura karin sojoji da yan sanda a fadin kasar a matakin martani ga hare haren da suka auku.

A birnin Paris an haramta dukkan wasu tarukan jama'a har zuwa ranar Alhamis, an kuma soke dukkan harkokin wasanni, hakannan an rufe dandalin Eifel Tower har sai abin da hali ya yi.

An kuma tsaurara tsaro a ofisoshin jakadanci da gine gine na hukumomin kasashen waje.

Asibitocin birnin Paris sun ce sun yiwa mutane 300 magani bayan aukuwar hare haraen, 80 daga cikin mutanen suna cikin matsanancin hali.

Jama'a a Paris suna ta yin layi domin bada gudunmawar jini.

Hakkin mallakar hoto EPA

15:17 Hukumomin Faransa sun ce sun sami paspo din Syria a kusa da gawar daya daga cikin yan bindigar da suka kai hari a Paris.

Kimanin mutane 80 suka rasu a wani wurin wasannin kade kade.

Tun da farko wasu yan bindiga sun yi luguden harsasai a wani gidan cin abinci a birnin na Paris.

Wasu maharan kuma sun tada bama bamai a wajen babban filin wasan kwallon kafa na Stade de France yayin da Faransa ke buga kwallo da Jamus.

14:20 Firayiministan Israila Benjamin Netanyahu yace kasarsa na tare da Faransa a yakin da ta ke yi da ayyukan ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Firayiministan Israila Benjamin Netanyahu

Shi ma shugaban Iran Hassan Rouhani ya baiyana harin a matsayin mummunan laifi akan bil Adama.

Hakan nan ya kuma soke ziyararsa zuwa Faransar.

Shugaban China Xi Jinping ya jajantawa Mr Hollande, ya kuma shaida masa cewa a shirye yake ya karfafa hadin kai domin yaki da ta'addanci.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya baiyana harin da cewa abin kaico ne

13:37 Faransa ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku domin jimamin mutanen da suka rasu a harin ta'adannaci a Paris. Magajiyar garin birnin Paris Anne Hidalgo ta ce birnin ya yi babban rashi dangane da hare haren yan ta'adda inda mahara suka kai hari wuraren da matasa kan ziyarta a karshen mako.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anne Hidalgo Magajiyar garin birnin Paris

13:01 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ya kadu matuka da harin ta'addanci da aka kai akan fararen hula wadanda basu ji ba basu gani a Paris.Buhari na NajeriyaBuhari ya mika ta'aziyya ga shugaban Faransa Francois Holland da kuma alummar Faransa baki daya.

Image caption Shugaba Buhari na Najeriya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Rasha Vladimir Putin

12:53 Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi Allah wadai da hare haren da aka kai Paris. Yace halayyar dabbancin yan ta'adda kalubale ne ga cigaban al'umma.

13:45 Kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci ta IS ta fitar da wata sanarwa inda ta dauki alhakin kai hare-haren da aka kai a Faransa wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla dari da ashirin da bakwai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Hollande ya nuna kaduwa

08:18 Ofishin Firayiministan Burtaniya ya ce Mista David Cameron zai jagoranci wani zama na gaggawa a kasar sakamakon hare-haren na Faransa.

07:12 Soke Tafiye-Tafiye

  • Shugaba Francois Hollande ya fasa halartar taron G20 a Turkiya saboda hare-haren kasarsa.
  • Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya fasa ziyarar da zai kai Italiya da Faransa.

06:55 Rahotanni a Paris na cewa uku daga cikin maharan sun tarwatsa kansu da bama bamai a cikin gidan rawa na Bataclan.

06:54 Suma kasashen Iran da Saudiya da Qatar da Rasha sun yi Allah awadai da hare-haren da aka kaddamar a Faransa.

06:28 Magajin Garin Paris ya bukaci mutane da su ci gaba da zama a cikin gida.

06:17 An kwashe wasu daga cikin wadanda suka tsira a hare-haren zuwa inda za kwantar musu da hankali.

Hakkin mallakar hoto Getty

06:14 'Yan sanda a Paris sun ce dukkan maharan da suka far ma birnin sun mutu.

05:36 Kamfanin dillancin labarai na AFP ya tsinkayi wasu jami'ai na cewa mahara 8 ne suka mutu, bakwai daga ciki, sun mutu ne ta hanyar tayar da bama-baman da ke daure a jikinsu.

04:45 Babban jami'i mai shigar da kara na gwamnatin Faransa ya tabbatar da mahara 7 a lamarin.

Hakkin mallakar hoto epa

04:35 Wata majiya a Faransa ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kimanin mutane 200 suka jikkata a hare-haren, kuma 80 daga ciki suna cikin mawuyacin yanayi.

04:26 Duk da dokar tabaci da Shugaba Hollande ya ayyana a fadin kasar, rahotanni sun ce jiragen sama dana kasa za su ci gaba da zirga-zirga.

03:38 A wani yanayi na alhinin hare-haren, an kunna wuta mai launin tutar Faransa a can saman a cibiyar kasuwanci ta duniya da ke New York.

03:24 Jaridar Le Parisien ta Faransa wadda ta tattara adadin mutanen da hare haren suka shafa, ta ce mutane 55 ne ke cikin mawuyacin hali.

03:02 Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren na Paris ya karu zuwa 140.

02:50 A sanadiyyar hare-haren, kasar Belgium to bullo da tsananta bincike a inda ta hada iyakoki da Faransa.

Hakkin mallakar hoto AFP

02:25 Shugaba Hollande lokacin da ya ziyarci gidan rawa na Bataclan inda harin yafi muni, ya ce za su yaki ta'addanci ba bu sani ba sabo.

02:14 Hukumomi a Faransa sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane 100 a hare-haren da aka bayyana mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan yakin duniya na 2.

02:07 An rufe iyakokin Faransa sakamakon munanan hare-haren.

Hakkin mallakar hoto AP

01:53 An girke karin sojoji 1,500 a birnin Paris bayan munanan hare-haren da aka kai.

01:38 Wasu majiyoyin 'yan sanda na nuna cewa kimanin mutane 100 ne suka mutu a gidan rawa na Bataclan.

01:32 Firayiministan Burtaniya David Cameron ya ce ya girgiza sosai da jin labarin hare-haren, sannan ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don taimaka wa Faransa.

Hakkin mallakar hoto AP

01:30 Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana hare-haren a matsayin wani yunkuri na addabar farar hula da basu ji basu gani ba.

01:20 Wasu shugabannin kasashen duniya sun yi Allah wadai da hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 40.

01:17 'Yan sanda sun tabbatar da cewa biyu daga cikin hare-haren, na kunar bakin wake ne, yayin da daya kuma, bom ne aka dasa.

01:07 'Yan sanda sun ce an kashe akalla biyu daga cikin maharan Bataclan.

Hakkin mallakar hoto AP

01:05 Shugaban Faransa Hollande ya ayyana dokar ta baci a fadin kasar, bayan hare-haren da aka kaddamar.

Hakkin mallakar hoto Reuters

01:00 Sauran wuraren da aka kai hare-haren sun hada da gidan rawa na Bataclan, da gidan abinci na Le Petit Cambodge, da kuma wajen dabdala na Le Carillon.

00:51 Shugaba Hollande ya bayar da umurnin a girke karin sojoji a birnin Paris inda aka kaddamar da hare-hare.

00:46 'Yan sanda a Paris sun danna cikin gidan rawa da ake garkuwa da akalla mutane 100.

00:43 An fitar da shugaba Hollande daga filin wasan, sannan aka dakatar da wasan, yayin da kowa ya watse.

Image caption Filin wasan da aka kaddamar da hari

00:25 Akalla mutane 60 a ke garkuwa da su a Paris din.

00:21 Rahotannin na cewa an kuma yi harbe harbe a wani gidan rawa dake gunduma ta 11 a birnin Paris.

00:15 Cikin wuraren da aka kaddamar da hare-haren har da filin wasa na kasar inda shugaba Francois Hollande ke kallon wasan kwallon kafa tsakanin kasarsa da Jamus.

00:09 Hare-haren da aka kaddamar a Faransa kawo yanzu, an tabbatar da mutuwar akalla mutane 40