Kananan yara na fama da tsaninin yunwa

Wasu mata da suka kai ziyara wasu sansanonin 'yan gudun Hijira a jihar Borno sun koka da irin mawuyacin halin da mazauna sansanonin ke ciki.

Kungiyar matan ta ce halin kunci da rashin lafiya da kuma karancin abinci mai gina jiki shi ne ya fi addabar mazauna sansanin, wadanda kusan dukkan su mata ne da kananan yara da aka kashe iyayensu.

Dr. Rahama Hasan na daya daga matan da suka kai ziyara sansanin Dalori a jihar Borno, kuma ta shaida wa BBC cewa jarirai ba sa samun wadataccen ruwa nono sannan wadanda suka girma ma ba su da isasshiyar lafiya.

'"An ce mana kungiyar UNICEF ce ke lura da wajen, amma ba sa barin magungunan da suka yi saura saboda gudun kada a sace magungunan", in ji Dr. Rahama

Ta kara da cewa 'yan gudun hijirar na bukatar abinci mai gina jiki da kuma ruwan sha da kuma sutura saboda sanyin hunturu.

Rikicin kungiyar Boko Haram dai ya raba mutane sama da miliyan biyu da gidajensu.