Sanatoci za su koyi amfani da Facebook

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saraki ya ce Facebook ne zai dauki nauyin horas da 'yan majalisar dattawan.

Kamfanin Facebook zai horas da 'yan majalisar dattawan Najeriya kan yadda ake yin amfani da shafin sada zumuntar.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban majalisar dattawan ta ce hakan zai bai wa 'yan majalisar damar isar da sakonninsu ga 'yan kasar ba tare da matsala ba.

A cewar shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki, mutane da dama na yi wa 'yan majalisar sojan-gona a shafukan sada zumunta, shi ya sa za a yi musu bita, sannan a "tantance" shafukansu domin kawar da matsalar.

Ya kara da cewa jami'an Facebook ne za su dauki nauyin koyar da 'yan majalisar dattawan, don haka majalisar ba za ta kashe ko sisi ba.