'Boko Haram na gab da zama tarihi'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya ce imma 'yan Boko Haram ba su san abinda ake nufi da Allahu Akbar ba, ko kuma ba su san Shi ba.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram na gab da zama tarihi, domin kuwa dakarun tsaro sun ci karfinta.

Shugaban ya bayya hakan ne a Yola babban birnin jihar Adamawa, a ranar Jumu'ah, yayin da ya kai ziyara domin duba halin da 'yan gudun hijira ke ciki, da kuma yanayin tsaro a yankin na arewa maso gabashin Nijeriya.

Shugaba Buhari ya kuma yi wa 'yan gudun hijira albishir da cewa, gwamnati za ta gyara masu garuruwansu nan bada jimawa ba, domin su koma gida.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da miliyan biyu da gidajensu.