IS ta dauki alhakin kai hare-haren Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci ta IS ta fitar da wata sanarwa inda ta dauki alhakin kai hare-haren da aka kai a Faransa wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla dari da ashirin da bakwai.

Shugaba Hollande na Faransa ya bayyana hare-haren a matsayin wani yunkuri na yaki da kungiyar IS ke kokarin yi.

Shugaban kasar ya kuma ayyana dokar ta baci a kasar.

Wasu 'yan bindiga guda takwas sun rasa rayukansu a yayin da suka kai hare-haren kunar bakin wake a wurare shida da aka kai harin a babban birnin Faransa.

Kusan mutane takwas ma sun rasa rayukansu a gidan rawa inda maharan suka kai harin.

Wani ganau ya ce maharan na ihu suna cewa suna daukar mataki ne a kan Faransa saboda matakin sojin da ta dauka a kan Syria.

Tun da farko 'yan bindigar sun ta harba harsashi ne a wani gidan cin abinci lamarin da ya janyo mutane da yawa suka samu raunuka wasu kuma suka mutu.

Sauran 'yan bindigar kuma da na bama-bamai suka yi a wajen babban filin wasan kasar inda Faransa ke buga wasan sada zumunta tare da kasar Jamus.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba