Za mu ci gaba da yakar kungiyar IS —Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Faransa ta lashi takobin ganin bayan mayakan IS

Faransa ta ce za ta ci gaba da yin luguden- wuta ta sama akan kungiyar mayakan IS a kasashen Syria da kuma Iraqi.

Kungiyar IS tace ita ke da alhakin hare -haren da aka kai birnin Paris, tana mai cewa martani ne ga yakin da Sojojin Faransan ke yi da kungiyar

Prime Ministan Faransa Manuel Valls, ya ce Faransa na cikin yaki a cikin gida da kuma a waje-- sannan ya ce za ta yi nasara.

Mutane 129 ne suka mutu, sannan mutane 350 suka sami raunuka a hare haren da aka kai a birnin Paris a ranar Jumu'ah