Oscar Pistorius ya fara aikin bautar kasa

Oscar Pistorius Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Oscar Pistorius

Kafofin yada labaran Afrika ta kudu sun ruwaito cewa dan tseren gudun nakasassun wanda ya sami lambar zinariya Oscar Pistorius ya fara aikin bautar kasa ta hidimar al'umma a yau tun bayan da aka sako shi daga kurkuku makonni uku da suka wuce.

An sako shi ne na wucin gadi bisa wasu sharudda a watan da ya gabata aka kuma yi masa daurin talala a kasa da shekara guda na wa'adin daurin shekaru biyar da aka yanke masa bisa kashe matarsa Reeva Steenkamp ba da gangan ba a shekarar 2013.

Lauyoyin gwamnati masu sun daukaka kara zuwa kotun koli ta Afirka ta kudu domin kalubalantar hukuncin da kuma bukatar sake mayar da shi gidan yari.