Mutane 13 sun mutu a Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu tayar da kayar baya na kungiyar Al-Shabab

Kungiyar Al-Shabab ta kai hari kan wata makarantar horar da sojoji da ke kudancin Somalia lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji a kalla goma sha uku.

Dakarun Somalia sun gwabza sosai da maharan har tsawon sa'oi uku kafin komai ya dai-daita a sansanin da ke kusa da birnin Kismayo da ke gabar ruwa.

Sojoji bakwai sun samu raunuka ya yin da a ka kashe masu tayar da kayar bayan su goma.

Kungiyar al-shabab dai na yaki da sojojin majalisar dinkin duniya wadanda ke goyon bayan gwamnati a Somalia, kuma a baya ta kai hare-hare da dama a Kenya makwabciyar kasar ta Somalia.