Ana zanga-zanga a Koriya ta Kudu

Image caption Masu zanga-zangar kin amincewa da manufofin gwamnati a kan ilimi

'Yan sanda sun gwabza da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Seoul babban birnin Koriya ta kudu, a yayin daya daga cikin zanga-zanga mafi girma da aka taba yi a birnin cikin shekaru masu yawa.

Tuni masu zanga-zangar suka kutsa ta cikin shingaye kana suka matsar da motocin 'yan sanda da aka toshe tituna da su.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun watsawa masu zanga-zangar ruwan zafi da kuma barkwanon tsohuwa.

Dubban mutane ne suka bi sahun masu zanga-zangar kin jinin gwamnati dangane da manufofin ta na a kan ayyuka da kuma ilimi.

Rahotanni sun ce an tsare akalla masu zanga-zanga goma.