Faransa:Wajibi a hada kai a yaki ta'addanci

Firayiministan Faransa Laurent Fabius
Image caption Firayiministan Faransa Laurent Fabius

Firayiministan Faransa Laurent Fabius Yana magana ne a Vienna gabanin zagaye na biyu na taron kasa da kasa wanda ya hada da masu taimakawa kungiyoyin da ke yaki a Syria.

Wakilin BBC yace babu wanda ke tsammanin samun wani cigaba a yau sannan kuma akwai rashin jituwa a game da makomar shugaba Bashar al Assad.

Fada tsakanin gwamnatin Syria da kungiyoyin yan tawaye da kuma masu da'awar jihadi ya hallaka mutane fiye da dubu dari biyu da hamsin a Syria cikin kusa da shekaru biyar.