Abubuwa 10 da aka sani a kan Harin Paris

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tarzomar ta fara ne jim kadan bayan karfe 9 na dare yayinda mutane ke shakatawa a daren juma'a a babban birnin kasar.

Wuraren da aka hara sun hada da mashaya da gidanjen abinci da wani gidan rawa da kuma wani wurin babban wasan kwallon kafa.

Harin da aka kai gidan rawa na Bataclan mai kujeru 1,500 shine mafi munin harin daren na ranar Juma'a.

Yan bindigar sun bude wuta a kan mutanen da suka je sauraron wakar kungiyar makadan rock na Amirka inda suka kashe a kalla mutane 80.

Kungiyar masu da'awar Jihadi ta fidda sanarwa a ranar Asabar ta na ikrarin daukar alhakin kai harin tare da cewa hare haren martani ne ga shigar Faransa na kai farmaki ta sama a kan mayakan IS a Syria da Iraqi.

Maharan takwas sun mutu.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya baiyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.

Mr Hollande ya daga matsayin barazanar tsaron zuwa matakin kololuwa ya kuma kafa dokar ta baci a kasa baki daya.

An rufe gine gine da dama na hukuma da kuma wurin wasanni na Disneyland a Paris, an kuma soke wasannin da aka shirya za a yi, sannan an haramta gudanar da manyan taruka har tsawon kwanaki biyar masu zuwa.

Wadannan su ne hare hare mafi muni a Faransa kuma karo na hudu tun yakin duniya na biyu da kasar ta sanya dokar ta baci. Na karshe da aka sa dokar ta baci shine lokacin wasu jerin zanga zanga a shekara ta 2005 a yankunan talakawa.