Myanmar- Zmu mika mulki ga Aung Suu Kyi

Shugabar 'yan adawa Aung San Suu Kyi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jam'iyyar NLD ce ta lashe zaben da aka yi a Myanmar.

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein ya yi wa al'umar kasar alkawarin zai mika mulki hannun shugabar jam'iyyar adawa Aung San Suu Kyi cikin lumana, bayan da jam'iyyarta ta lahe zaben da aka gudanar.

Shugaba Thein ya yi wannan jawabi ne a wani taron siyasa da aka gudanar da Yanglon.

Jam'iyyar National League for Democracy ta lashe kashi 80 cikin 100 na kujerun majalisun dokokin kasar a zaben da aka yi a makon da ya wuce.

Ana kuma sa ran za a tattauna akan samar da sabuwar gwamnati a farkon mako mai zuwa.

Idan har aka mika mulkin, wannan zai kawo karshen mulkin da sojoji ke marawa baya na shekaru hamsin da aka yi a kasar ta Myanmar.