Paris- An sake gano wata motar

Haris da aka kai birnin Paris Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 129 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a ranar Juma'a.

'Yan sanda a kasar Faransa sun sake gano mota ta biyu da ake kyautata zaton an yi amfani da ita a harin da aka kai birnin Paris a ranar juma'a da ta wuce.

An gano bakar kujerar da ke bayan motar a wajen garin birnin, wadda rahotanni suka bayyana cewa an ga makamai a cikinta.

A jiya asabar, an gano wata mota da aka yi hayarta daga kasar Jamus a kusa da dakin taron da yawancin mutane 129 da suka rasu.

Jami'an tsaro sun kuma kama wasu mutane uku a Brussels da ake zaton su na da hannu a kai harin.

Daya daga cikin mutane bakwai da ake zargi da kai harin wani bafarashe ne mai suna Omar Ismail Mostefai, wanda akai masa shaidar ya na da tsattsauran ra'ayin addinin musulunci.

A bangare guda kuma 'yan sanda na yi wa abokai da 'yan uwan Mustefai tambayoyi a kan shi.