An gano kabari makare da gawawwaki a Iraqi

Kabarin da gano a yankin Sinjar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A makon da ya wuce an gano wani kabarin makare da gawawwakin mta tamanin.

An gano wani kabari a garin Sinjar da ke arewacin kasar Iraqi, inda mayaka Kurdawa suka karbe daga hannun masu tada kayar baya na kungiyar IS a ranar Juma'a da ta wuce.

Ganau kan lamarin sun shaidawa BBC cewa an gano kusan gawawwaki hamsin a bincike na baya-bayan nan da aka yi a wurin.

A jiya asabar ne jami'an Kurdawa suka sanar da gano wani kabari da makare da kusan gawawwaki tamanin dukkan su mata.

Garin dai ya na da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Yazidi marasa rinjaye.

Ya yin da mayakan IS ke kallon garin a matsayin mai cike da tarihi, ya yin da suka cafke wasu daga cikin da hallaka da dama.