An kara matakan tsaro a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Cameron ya sha alwashin yaki da IS.

Firai Ministan Biritaniya, David Cameron, ya ce an kara kudi a bangaren tsaron kasar domin murkushe duk wata barazana daga kungiyar IS mai ikirarin kishin Musulinci.

Mista Cameron ya ce kudin zai bai wa hukumomin tsaron kasar --- wadanda suka hada da (MI5, MI6 and GCHQ) -- kara daukar sabbin ma'aikata 1900.

A hirarsa da BBC, Firai Ministan na Biritaniya, ya yi gargadin cewa za a iya kai wa kasarsa hare-hare irin wadanda aka kai a Faransa ranar Juma'a.

Mr Cameron ya ce Biritaniya za ta ci gaba da daukar matakan tsaro a kan iyakokinta, sannan ta karfafa samar da bayanan sirri tsakaninta da sauran kasashen Turai a yakin da suke yi da kungiyar IS.