An gano gawarwakin 'yan ci rani a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai wasu 'yan ci rani da suka jikkata zuwa asibitin da ke birnin Al Arish

Jami'ai a Masar sun ce 'yan sanda sun gano gawarwakin 'yan ci ranin Afrika 15 wadanda alamu suka nuna cewa an harbe su ne da bindiga a yankin Sinai da ke areawacin kasar.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce yawancin mutanen 'yan Sudan ne. Har yanzu dai ba a gano wadanda suka kashe mutanen ba, kusa da garin Rafah a kan iyakar Gaza.

Ana samun karuwar tashin hankali a yankin, inda sojojin Masar suke kokarin murkushe kungiyar IS.

A ranar Lahadi ma an samu wasu 'yan ci rani takwas da ransu amma sun ji raunuka.

"Zafafa hare-hare"

Masu da'awar jihadi da ke yankin Sinai sun zafafa kai hare-hare tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi a watan Yulin 2013.

Tun a watan Oktobar 2014 aka sanya dokar ta baci a yankin, sakamakon wani hari da wata kungiya mai alaka da IS a yankin ta kai.

Ba a tabbatar da cewa ko kisan wadannan 'yan ci rani na da alaka da rashin kwanciyar hankalin da yankin ke fuskanta ba.