'Buhari ya nakasa arzikin Nigeria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Wasu masu hada-hadar hannun jari a Najeriya sun dora wa shugaban kasar, Muhammadu Buhari alhakin tawayar da tattalin arzikin kasar ya samu.

Mutanen -- wadanda suka ce sun yi asarar sama da Naira tiriliyan daya a kasuwar hada-hadar ta hannun jari a tsawon watanni biyar -- sun alakanta hakan da tsaikon da gwamnatin Buhari ta yi kafin ta nada ministoci.

Wani mai kamfanin hada-hadar hannun jari a jihar Legas, Malam Kasimu Garba Kurfi, ya shaida wa BBC cewa rashin nadin ministocin da wuri ne ummul-aba'isin hana shigowar masu zuba jari kasar domin sun kasa fahimtar inda tattalin arzikin kasar ya sanya gaba.

Sai dai kuma wani masana tattalin arziki a Najeriyar, Alhaji Shu'aibu Idris, ya ce faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ne ya shafi tattalin arziki da kuma darajar kudin kasar.

Da ma dai shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya fito fili ya fadi cewa kasar tasa tana fuskantar matsalar tattalin arziki.