Rashin kudi kan iya kawo cikas ga Birtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC CHINESE

Kwamitin kimiya da fasaha na Majalisar wakilan Birtaniya na duba yuwar ko za a iya tattara bayyanai a kan masu amfani da shafukan internet.

Maganar ta taso ne ya yinda mutane ke neman karin haske a kan yawan kudin da gwamnati za ta kashe domin shirin ya gudana.

A makon daya gabata ne aka zartar kudurin binciken da aka yi wa lakabi da IP wanda zai sa a samarwa 'yan sanda da masu leken asiri da horo a kan yadda zasu inganta ayuikansu wajen yaki da masu aikata miyagun laifuka da ta'adanci da kuma sauran danyen ayuika.

Kudurin zai ba jamian tsaro damar nadar bayanai kan duk wani dan Birtaniya da ke amfani da shafuka internet.

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta samar da fam miliyan 175 nan shekaru goma masu zuwa domin tattara bayanai tare kuma da adanasu .