Ana tuhumar wasu kan bautar da dan Nigeria

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan sandan Biritaniya a bakin aiki.

Wata kotu a Biritaniya tana tuhumar wani Likita da wata ma'aikaciyar jinya mazauna Biritaniya kan ajiye wani dan Najeriya tare da bautar da shi a gidansu na tsawon shekara 24.

Wata kotu a birnin London ta samu labarin cewa an shigar da mutumin Biritaniya ba bisa ka'ida ba tun yana dan shekara 14 tare da yi masa alkawarin bashi ilimi.

Amma sai Emmanuel da Antan Edet suka kwace fasfo dinsa suka kuma ce masa za a mayar da shi kasarsa idan ya gaya wa 'yan sanda.

A ranar Laraba ne za a yanke musu hukunci.