An bayar da umarnin kama Sambo Dasuki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin yin yaki da ta'addanci da karbar hanci da rashawa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni a kama, sannan a hukunta tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki da duk mutanen da aka samu da hannu a badakalar sayen makamai domin yaki da ta'addanci daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin ne bayan da ya karbi kwarya-kwaryar rahoton kwamitin da ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro ya kafa domin yin bincike kan lamarin.

Sai dai Kanar Dasuki ya musanta zargin, yana mai cewa kwamitin bai gayyace shi domin jin ta bakinsa ba.

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa kan yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, ya ce kwamitin ya gano cewa kimanin Naira biliyan 644 sun yi batan-dabo daga hannun Kanar Dasuki da sauran mutanen da ake tuhuma.

A cewar sa, "Kwamitin ya gano cewa an bayar da kwangila 513 a kan $8,356,525,184.32; N2,189,265,724,404.55 and €54,000.00; A cikin kwangilolin, ba a aiwatar da guda 53 wadanda kudinsu ya kai $2,378,939,066.27 da N13,729,342,329.87".

Adesina ya kara da cewa binciken da kwamitin ya yi ya nuna cewa "Tsakanin watan Maris na shekarar 2012 da watan Maris na shekarar 2015 Kanar Sambo Dasuk ya bayar da kwangiloli na bogi da suka kai N2,219,188,609.50, $1,671,742,613.58 da €9,905,477.00. An ce za a sayo jirage hudu samfurin Alpha Jets, da jirage masu saukar ungulu 12, da bama-bamai da alburusai, sai dai ba a sayo su ba, ballatanta a mika su ga rundunar sojin saman Najeriya".

Ana dai zargin Kanar Sambo Dasuki ne da karkatar da akalar kudaden da aka ware wa harkar ta tsaro.

Gwamnatocin baya dai sun fitar da makudan kudade domin sayen makamai da jiragen yaki amma sai ga shi ba a ga inda wadannan makaman da jiragen suke ba.