Buhari zai bai wa Manoma tallafi

Image caption Manoma dai su ne suka fi kowa yawa a Najeriya.

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri na bai wa manoman shinkafa na kasar tallafin bashin kudi naira biliyan 20 a jihar Kebbi.

Shirin bayar da bashin wanda babban banki Najeriya CBN ya bullo da shi an samar da shi ne domin taimaka wa manoman shinkafar wajen bunkasa harkar noma a kasar.

Shugaban CBN Godwin Emefiele ya ce rashin samun ingantaccen iri da kayan noma na zamani da kuma rashin tallafi na daga cikin abubuwan da ke nakasa harkar noma a kasar.

Shugaba Buhari ya ce "mun yi sakaci tun lokacin da muka watsar da harkar noma saboda samun man fetur, yanzu kuwa lokaci ya yi da za mu koma gona."

"Manoma sun koka"

Yawanci manoman kasar sun bayyana fargabar cewa tallafin bashin da gwamnatin shugaba Buhari take shirin ba su ka iya zama irin abin da ake cewa rijiya ta bayar da ruwa amma guga ya hana.

Manoman dai sun nemi gwamnatin da ta sanya ido sosai domin ganin cewa wadanda aka nufa da bashin ya kai gare su.

Shinkafa dai ta kasance wani muhimmin abinci a Najeriya saboda irin albarkatun kasar da Allah ya huwace wa kasar na nomanta.

Sai dai kuma kasar na sahun gaba-gaba wajen fasakaurin shinkafar daga kasashen waje.