'Rijiya ka iya ba da ruwa guga ya hana'

Image caption Manoma dai su ne suka fi kowa yawa a Najeriya.

Manoma a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na bayyana fargabar cewa tallafin bashin da gwamnatin shugaba Buhari take shirin ba su ka iya zama irin abin da ake cewa rijiya ta bayar da ruwa amma guga sai ya hana.

A ranar Talata nan ne dai shugaba Buhari zai kaddamar da wani shirin ba wa manoma tallafin bashi domin bunkasa noman shinkafa a kasar.

Babban bankin kasar ne wato CBN yake jagorantar shirin.

Manoman dai sun nemi gwamnatin da ta sanya ido sosai domin ganin cewa wadanda aka nufa da bashin ya kai gare su.

Shinkafa dai ta kasance wani muhimmin abinci a Najeriya saboda irin albarkatun kasar da Allah ya huwace wa kasar na nomanta.

Sai dai kuma kasar na sahun gaba-gaba wajen fasakaurin shinkafar daga kasashen waje.