CAR: Mutane na shakkar jami'an wanzar da zaman lafiya

Al'ummar jumhuriyar tsakiyar Afrika
Image caption Al'ummar jumhuriyar tsakiyar Afrika

Wani sabon rahoto ya ce al'ummar kasar Africa ta tsakiya suna zaune cikin zama irin na zulumi, har ma takai su ga mika wuya ga mayakan sa-kai domin neman su kare su.

Rahoton wanda cibiyar ci gaban kasashen ketare ta Birtaniya ta Overseas Development Institute ta wallafa, ya ce yanzu haka mutane sun kasance suna shakkar rundunonin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa.

Majalisar dinkin duniya ta zargi kungiyoyin mayakan sa-kai na musulmai da na kiristoci bisa mafi yawancin cin zarafin dan adam din da aka yi a kasar.

Sai dai kuma cibiyar ta ce mutanen da ta gana da su sun bayyana cewa sun fi hankalinsu ya fi kwanciya da kungiyoyin mayakan sa-kan akan sojojin wanzar da zaman lafiya.