Gwamnoni na taro kan Biafra

Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Nnamdi Kanu shi ne jagoran masu kokarin ganin an kafa jamhuriyyar Biafra.

Gwamnonin jihohin kudu maso gabashin Najeriya suna taro a ranar Talata a Enugu, domin tattaunawa kan yadda za su nemo mafita ga zanga-zangar da matasa ke yi a yankin a kokarinsu na ganin an kafa jamhuriyyar Biafra.

Matasan na yin zanga-zangar ta baya-bayan nan ne a jihohin da ke kan iyaka da yankin kudu maso kudancin kasar mai arzikin man fetur.

Rundunar sojin Najeriya wadda a yanzu haka suke fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram a arewacin kasar, sun yi barazanar murkushe masu zanga-zangar wajen yin amfani da karfin da bai wuce kima ba, suna masu danganta masu zanga-zangar da masu son ganin ballewar Najeriya.

Shekaru 40 da suka gabata ne aka shafe shekaru uku ana yakin basasar neman kafa jamhuriyyar Biafra karkashin jagorancin Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu.