An sallami jaririn da ya kamu da Ebola

Kwayar cutar ebola Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwayar cutar ebola

Jami'an lafiya a Guinea sun ce wani jariri wanda shi ne mutum na karshe mai dauke da cutar Ebola ya warke kuma an sallame shi daga wurin da ake kula da shi, a Conakry, babban birnin kasar.

Mai magana da yawun cibiyar kula da masu cutar ta Ebola ya ce gwaje-gwajen da aka yi guda biyu akan jaririn sun nuna ba ya dauke da cutar.

Za a dai a ayyana kasar ta Guinea a matsayin wadda mutanenta ba sa dauke da cutar Ebola idan har ba a kara samun mai dauke da cutar ba nan da makwanni 6.

Tuni dai aka ayyana kasashen Saliyo da Laberiya masu makwabtaka da Guinin a matsayin wadanda ba su da cutar.