Batirin waya mai saurin caji na Huawei

Image caption Sabon batirin kamfanin Huawei

Kamfanin kasar China na Huawei ya fito da wasu tagwayen batiran caja waya a cikin 'yan mintuna kadan.

Batiran dai sun hada da mai gajere da dogon zango samfirin Lithium-ion kuma ana amfani da caja mai kuttu samfirin bespoke.

Za a iya caza batiri mai gajeren zangon har zuwa kaso 68 a cikin minti biyu.

Shi kuma mai dogon zango zai iya cazuwa a da kaso 48 a cikin minti biyar.

Kamfanin na Huawei ya ce kaso 48 din na batirin mai dogon zango zai iya dadewa har na tsawon awonni goma na magana.

Yanzu haka kamfanoni na ta kokarin kirkiro irin wannan batirin.

Ko a watan Maris ma sai da kamfanin Samsung ya sanar da cewa batiran da sabuwar wayar kamfanin ta Galaxy S6 za ta iya shafe awonni hudu cir bayan samun caji na minti 10.

Haka shi ma kamfanin kasar Isra'ila mai suna Storedot ya kaddamar da wata fasahar cajin waya cikin dan lokacin kankani a farkon shekarar 2015.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sauran kamfanoni suna son su ma su fito da wannan fasahar

Ana kuma sa ran cewa fasahar za ta iya caza batirin wayar komai-da-ruwanka ta smartphone a kasa da minti daya kacal.