IS na shirin kai wa Birtaniya hari

Mayakan kungiyar IS sun soma kokarin kai wa shafukan internet na wasu wurare a Birtaniya hari.

Wasu daga cikin wuraren da mayakan IS ke kokarin satar bayyanansu ciki har da asibitoci da fanin masu kula da zirga zirgar jiragen sama a cewar sakataren kudi na kasar George Osborne.

Mr Osborne ya ce gwamnati ta soma shirin rubunya kudin da aka ware wa shirin yaki da masu satar bayyanai zuwa fam biliyan 1.9 nan da shekaru biyar masu zuwa.

Bayyanan Mr Osborne na zuwa a dai dai lokacin da kungiyar IS ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai hare haren birnin Paris a ranar Juma'a.

A wani labarin kuma ma'aikatar tsaro ta Birtaniya ta ce sojojin kasar sun kai wa wani gungu na mayakan kungiyar IS hari a kasar Iraki a ranar Litini.