Kano: Ana tuhumar mutane 57 kan fyade

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun sha kama mutanen da ake zargi da yin fyade.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta gurfanar da wasu mutane 57 da ake zargi da yi wa yara fyade.

Kotunan da aka gurfanar da mutanen dai sun yi umarnin a ci gaba da tsare su a gidan kurkuku.

Sai dai fa wadanda ake zargi din sun musanta tuhumar da ake yi musu.

Jihar dai na daya daga cikin jihohin da matsalar fyade ta yi yawa.