Kamfanin Ford ya kera motar farko a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne karo na farko da kamfanin ya kera mota a Najeriya.

Kamfanin kera motoci na Amurka Ford, ya kaddamar da motarsa ta farko a sabon reshensa da ke Najeriya.

Da farko dai an tsara cewa kamfanin wanda ke kusa da jihar Lagos, zai samar da motocin akori-kura guda 10 samfurin Ranger kowacce rana, domin sayar wa a Najeriya.

Shugaban kamfanin na kasashen da ke kudu da hamadar sahara Jeff Nemeth, ya ce suna sa ran samun alheri sosai a sabuwar kasuwar ta Afrika.

Har I zuwa yanzu dai kamfanin na samar da motocinsa na Fordi ne a Afrika ta kudu kawai, inda yake kera ababen hawa 85,000 kowacce shekara don sayarwa a kasashe 24 na Afrika