Dan Nigeria ya warware lissafi mai sarkakiya

Hakkin mallakar hoto Opeyemi Eno
Image caption Dr Opeyemi Enoch, wanda warware wani lissafi mai suna Riemann Hypothesis.

Wani malamin jami'a a Najeriya Dokta Opeyemi Enoch, ya warware wani lissafi mai suna Riemann Hypothesis wanda aka kasa warware shi tsawon shekaru fiye da 150.

Malamin wanda yake koyar da lissafi a jami'ar gwamnatin tarayya dake Oye-Ekiti dai zai samu kyautar dalar Amurka miliyan guda.

Wata sanarwar daga jami'ar tace, malamin ya gabatar da yadda ya warware lissafin ne yayin wani babban taro na masana lissafi da ilimin komfuta da aka yi a birnin Vienna na kasar Austria.

A baya dai an sha samun wasu suna irin wannan ikirari na nuna hazaka a Najeriya.