Me ya sa harin Faransa ya dauki hankali?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane 139 ne dai suka mutu a harin na ranar Juma'a

Masu sharhi a Najeriya na alakanta irin yadda harin ta'addanci da aka kai Faransa ranar Juma'a, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane139, ya dauki hankalin duniya da wasu dalilai guda uku.

Dalilin farko dai shi ne kafafen yada labarai na rediyo da talbijin da ma kafofin sadarwa na zamani kamar Facebook da Twitter da Google da dai sauransu duka mallakar turawa ne.

Haka kuma sun ce alakar kasashen turai da sauran kasashen duniya -- musamman a nahiyar Afirka wadda turawa suka yi wa mulkin mallaka -- sun taimaka wajen kwakwazon batun hare-hare a nahiyar turai.

Dalili na uku da masu sharhin suka bayar shi ne irin yadda shugabannin kasashen turai suke nuna damuwarsu da 'yan kasarsu sabanin kasashen Afrika.

Tun dai bayan harin da aka kai wa Faransa 'yan Najeriya da sauran kasashen Afirka suke ta mayar da martanin tare da muhawara, musamman a kafofin sadarwa na zamani.

Mutane da dama dai na bayyana ra'ayinsu ne a kan yadda shugabannin kasashe da na kamfanoni na duniya suka rika mai da martani a kan hare-haren na birnin Paris, alhalin wasu makamantansu ko ma wadanda suka fi su muni sun faru a Afirka, amma ba a kula da su kamar haka ba.