Rasha ta kai hare-hare kan IS a Syria

Hakkin mallakar hoto SYRIA REBELS GATHERING
Image caption Hare-haren da Rasha ke kaiwa kan 'Yan kungiyar IS

Rasha ta ce ta kai munanan hare-hare kan sansanonin'yan kungiyar IS a Syria.

Ministan tsaron kasar Sergei Shoigu ya tabbatar da cewa Rasha ta yi amfani da manyan makamai wajen kai hare-haren.

Ya cigaba da cewa jiragen yakin su sun harba makamai masu linzami a dai-dai inda masu tayar da kayar bayan su ke a Raqqa da Deir ez-Zor da ke gabashin Syria.

Tunda farko, Shugaba Putin ya sha alwashin daukar fansa kan kungiyar ta ISIS bayanda shugaban hukumar tsaron Rasha ya tabbatar da cewar yan ta'adda ne suka harbo jirgin rashan nan da ya fadi a yankin Sinai na kasar Masar a watan jiya , lamarin da yayi sanadiyar mutuwar dukkanin mutane 224 da ke cikin jirigin.