Coci ta ki binne wadanda take bi bashi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majami'ar methodist

An soki lamirin majami'ar Methodist a kudancin Afrika saboda kin binne mutanen da ta ke bi bashi.

Wata kungiya da ke bincike a kan ayyukan majami'u da 'yancin mutane ce ta yi allawadai da wannan mataki da majami'ar ta dauka na azabtar da wadanta ta kira talakawa.

Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da jama'a suka kai a kan wani tsari da suke biyan wani abu a duk wata ga cocin.

Sai dai kuma cocin wanda yana daya daga cikin majami'u mafi girma a Afrika, ya ce yana karbar wadannan kudade ne da nufin karfafa gwiwar mutane akan yin kyauta ko sadaka.